(ABNA24.com) Shugaban hukumar rayawa da kuma bunkasa al-adun musulunci a nan Iran Abuzar Ebrahimi Turkaman ya jaddada bukatar ci gaba da tarurruka na kusato da manya-manyan addinan duniya biyu, wato Musulmi da Kirista don samar da zaman lafiya a duniya.
Kamfanin dillancin labaran Iran Press ya nakalto Ebrahimi yana fadar haka a lokacinda yake ganawa da shugaban majalisar tattaunawa tsakanin addinai ta Vatikan Cardinal Miguel Ángel Ayuso Guixot wanda yake halattan taron tattaunawa tsakanin addinai wanda yake gudana a halin yanzu a nan birnin Tehran.
Tun shekara ta 1994 ne aka fara taro tsakanin kasar Iran da kuma Vatican, kuma ana gudanar da tarurrukan ne a ko wace shekara a iran ko a Vatican. Sannan taron da ke kudana a halin yanzu a nan Tehran shi ne na 11 tun lokacin da aka fara.
A jiya 11 ga watan Nuwamba ne aka fara taron a nan birnin Tehran, sannan za’a kammala shi a yau Talata.
/129
13 Nuwamba 2019 - 06:08
Lambar labari: 987581
Shugaban hukumar rayawa da kuma bunkasa al-adun musulunci a nan Iran Abuzar Ebrahimi Turkaman ya jaddada bukatar ci gaba da tarurruka na kusato da manya-manyan addinan duniya biyu, wato Musulmi da Kirista don samar da zaman lafiya a duniya.